Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Hossein Amir-Abdollahian, ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis cewa, rikicin Ukraine ya samo asali ne daga ayyukan tsokana na kungiyar tsaro ta NATO, a daidai lokacin da Rasha ta kaddamar da farmakin soji kan Ukraine.
Amma babban jami’in diflomatisyya na Iran, ya ce “Ba ma ganin daukar yaki a matsayin mafita, ya kamata a nemi hanyar tsagaita bude wuta’’
342/